19 Mayu 2026 - 12:08
Source: ABNA24
Jami'ai: 'Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai 39 Kuma Suka Kashe Malami A Jihar Oyo A Najeriya

Hukumomin Najeriya sun bayyana a jiya Litinin cewa 'yan bindiga sun sace akalla ɗalibai 39 da malamai bakwai a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, suka kashe daya daga cikin malaman, tare da raunata jami'an tsaro ta hanyar amfani da bama-bamai a lokacin ƙoƙarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jami'ai sun ce harin ya faru ne a ranar Juma'a a garin Ahoru Isinil a karamar hukumar Orire, inda aka kai hari kan makarantu da dama, ciki har da wata makarantar sakandire da makarantun firamare biyu. Gwamna Seyi Makinde ya ce an kashe daya daga cikin malaman da aka sace a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya yi nuni da wani faifan bidiyo. Ya kara da cewa an kama wasu mutane shida da ake zargi. Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan da ya bayyana a matsayin "Harin Wulakanci," kuma ya ce hukumomin tarayya suna aiki tare da jihar don ceto duk wadanda aka sace.

Sace-sacen gama-gari da ƙungiyoyin 'yan bindiga ke yi ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya a cikin 'yan shekarun da suka gabata; inda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke cin gajiyar rashin tsaro da iyakoki masu saurin keta su don kai wa matafiya, ɗalibai da al'ummomin karkara hari domin neman kuɗi da biyan biyan kudaden fansa.

……………………………………………………………………

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha